Wannan ya biyo bayan matsayar da kakakain Mjalisar Wakilai Femi Gbajabiamiala ya dauka na kauracewa sanya hannu kan kasafin kudin badi sai gwamnati ta biya diyya ga wadanda cin zarafin 'yan sandan SARS da aka rushe ya shafa.
In za a tuna Gbajabiamiala a jawabi gaban zauren majalisar ya ce ba zai sa hannu kan kasafin kudin ba sai ya kunshi diyya ga wadanda cin zarafin 'yan sanda a shekaru goma da suka wuce ya rutsa da su.
Wannan lamari ya samu kambamawar neman diyyar Naira tirilyan daya ga mutanen da suka ta da tarzomar daga Legas da hakan ya kai ga rushe rundunar SARS ya kuma juye zuwa ‘yar tsamar bangaranci.
Attahiru Bafarawa ya ce ba ya ganin laifin biyan diyyar da Gbajabiamiala ya nema, amma hakan ya hada da na yankin arewa.
Nan take shi ma dattijon kungiyar Miyetti Allah ta makiyaya Dodo Oroji ya ce makiyaya na bukatar samun diyyar shanunsu da a ka sace musamman a arewa maso yamma.
Zuwa yanzu dai gwamnatin Buhari da majalisar ba su maida martani kan wadannan bukatun ba, inda maimakon hakan shugaban ya bukaci matasa su ci amfanin shirye-shiryen sa na tallafi da su ka hada da NPOWER, Tradermoni,market moni da sauran su wadanda ya ce ba gwamnatin da ta taba tabukawa kamar gwamnatinsa ta APC ta wannan bangaren.