AREWA A YAU: Yadda Sana’o’in Hannu Da Sauran Ayyukan Dogaro Da Kai Ke Taimaka Wa Matasa - Satumba 27, 2023

Nasiru Adamu

Koyon kira, saka, sassaka da aikin kafinta na daga cikin hanyoyin da ko da matasa ba su samu aikin gwamnati ba zasu zama masu dogaro da kai har ma su taimaka wa sauran dangi.

Kungiyar INGAUSA da kan koyar da sana’ar fasaha ta amfani da harshen Hausa don fahimtar da wadanda iliminsu bai yi nisa ba, ta koya wa matasa sana’a, yanzu wasunsu suna daukar aiki.

Injiniya Mustapha Habu Rigim da ke jagorantar kungiyar ya ce nasarar da suka cimma na da yawan gaske.

Saurari shirin da Nasiru Adamu El-hikaya ya gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU: Yadda Sana’o’in Hannu Da Sauran Ayyukan Dogaro Da Kai Ke Taimaka Wa Matasa