AREWA A YAU: Bitar Wasu Daga Darussan Da Shirin Ya Tabo a Shekarar 2023 - Disamba 20, 2023

Nasiru Adamu El-Hikaya Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Sabon shirin AREWA A YAU zai yi bitar wasu daga darussan da shirin ya tabo a shekarar nan ta 2023 mai bankwana. Daya daga shirye-shiryen shi ne dokar amincewa da kafa hukumar kula da almajirai da tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari ta yi ta na jajiberin sauka daga mulki a karshen watan Mayu.

Wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El-Hikaya, ya shiga jihar Yobe don jin matakan bin kadun daliban jihar da su ka dawo daga Sudan bayan barkewar fitinar da ta birkita kasar.

Ko ba a ce dukkan almajirai 'yan arewacin Najeriya ba ne, amma a kullum a na ganin yara kanana na ragaita a kan tituna su na neman na kalaci da sauran su.

Alkaluma sun nuna akwai kimanin yara sama da miliyan 18 da ke gararamba a kan titunan arewacin Najeriya ba tare da samun kulawa ba.

Saurari shirin a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU