Tuni kwararru suka shiga jihohi a dukkan sassa uku na arewacin Najeriya da karfafa wa matasa gwiwa su shiga fasahar zamani maimakon dagewa sai sun samu ayyukan gwamnati.
Hakanan shirin zai leka gabashin Sokoto don duba yanda kafa cibiyoyin fasaha ke daukar hankalin masu sharhi.
Dr. Grema Kyari ne shugaban kwararrun fasahar zamani AI Technolnogy da a baya ya shigo shirin nan, inda ya bayyana yanda su ka tsara ratsa yankunan arewa don zaburar da matasa.
Mai sharhi kan lamuran yau da kullum daga Sokoto ta gabas, Muhammad Shu'aibu Bakwai, ya ce daya daga dattawan yankin Injiniya Ibrahim Gobir ne ya taimaka masu wajen samun cibiyoyin yanar gizo guda 4.
Saurari shirin:
Dandalin Mu Tattauna