AREWA A YAU: Tattaunawa Kan Matsalar Tsaro, Satumba 28, 2022

Nasiru Adamu El Hikaya

Shirin na wannan makon ya dora a inda ya tsaya a makon da ya gabata game da batun tsaro.

ABUJA, NIGERIA - Satar mutane don neman kudin fansa da sauran manyan lafuffuka da suka zama ruwan dare a jihohin arewacin Najeriya na ci gaba da yin barazana ga rayuka da dukiyar jama’a.

Nasiru Adamu Elhikaya ya ci gaba da tattaunawa da Dr. Ahmed Gumi kan yadda za a magance matsalar. Bayan haka ya tattauna da tsohon Darakta a fadar gwamnatin Najeriya Ahmed Ibrahim Lau, game da rawar da sarakunan gargaji suka taka a baya wajen kula da al’umma.

Saurari cikakken shirin da Nasiru Adamu Elhikaya ya gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU: Tattaunawa Kan Matsalar Tsaro, Satumba 28, 2022