AREWA A YAU: Tattaunawa Kan Hanyoyin Dawo Da Zaman Lafiya Da Hadin Kan Al'umma, Oktoba 5, 2022

Nasiru Adamu El Hikaya

Shirin ya tattauna da Ahmed Ibrahim Lau da kuma shugaban kungiyar fataken masara ta yankin arewa Modibbo Sadik Nafada.

ABUJA, NIGERIA - Shirin na wannan makon ya tattauna kan hanyoyin da za a dawo da zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummar arewa da aka ci gajiyar hakan a zamanin da ya shude da ma gabanin zuwan turawan mulkin mallaka.

Shirin ya kuma tabo bangaren tarihi, tattalin arziki, da zaman tare da duk suka karfafa a zamanin baya ta hanyar jagororin gargajiya da suka dora yankin kan turbar da a ke tunawa da ita ta nasara.

Saurari cikakken shirin Nasiru Adamu Elhikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU: Tattaunawa Kan Hanyoyin Dawo Da Zaman Lafiya Da Hadin Kan Al'umma, Oktoba 5, 2022