Sabon shirin arewa a yau ya duba yadda tarihin soke makarantu masu ba da takardar malunta mai daraja ta biyu ya jawo koma baya ga yanayin koyarwa a arewa da kyakkyawar alakar malamai a matsayin iyaye, dalibai a matsayin 'ya'ya.
Tsohon ministan ilimi a zamanin mulkin soja kuma Farfesan farko na ilimi a Najeriya Babatunde Fafunwa ne ya kawo tsarin da ya soke makarantun, inda a madadin haka aka karfafa makarantu masu ba da shaidar malunta mai daraja ta I wato NCE.
A gefe guda kuma, Haruna Aliyu Ningi ya ja hankali kan yadda matasan arewa ke amfani da yanar gizo wajen shagali da hotuna abin da ya sha bamban da yadda 'yan kudu kan tallata hajarsu da shirya wasu ayyuka masu kawo kudin shiga in aka debe 'yan damfarar yanar gizo daga cikinsu.
Dan gwagwarmaya daga arewa Abdulhamid Dankyarko wanda ya yi karatu a kwalejojin ilimi masu ba da shaidar malunta mai darata ta 2, ya tuna yadda tsarin makarantun suke a arewa.
Saurari shirin:
Your browser doesn’t support HTML5