Sabon shirin Arewa a Yau ya duba yadda ya dace alkiblar arewa ta kasance ta fuskar shirya hanyoyi na gari da za a ci gajiya bayan akasin da aka samu na kaucewa karantarwar iyayen yankin.
Hakika shiryawa damina tun rani kan ba manomi damar sanin abin da zai shuka don girbar ribar kwazonsa.
Yankin arewa na da albarkar noma da kiwo da kuma sana’o’in hannu kama daga kira, jima, sassaka, saka da sauransu.
Shahararren mai baituka Haruna Aliyu Ningi ya rubuta wata kasida da ya zaga da ita wajen wasu ginshikan yankin don su zama da amfani hatta ga na baya. Shin ya kwashe nikan da waka?
Talban Bauchi Tahir Ibrahim Tahir ya kawo mana karashen bayanansa kan arewa da muradunta da kan so a yi musu bita don kaucewa barin baya da kura.
Saurari shirin:
Dandalin Mu Tattauna