Abuja, Najeriya —
Shirin ya duba muhimmancin koya wa makiyaya da ma mata da matasansu wasu sana’o’in waje da kiwo da hakan zai ba su zabin samun karin hanyoyin samun kudin shiga.
Hakika idan makiyaya su ka samu sana’o’i na daban hakan zai taimaka ma wasunsu wajen kauce wa fadawa cikin miyagun laifuka lokacin da shanunsu su ka kare.
Wasu makiyayan kan ba da dalilan shiga miyagun laifuka kan rashin wata sana’ar baya ga kiwo kuma wasu dalilai sun sa sun rasa dukkan dukiyarsu ta shanu da su kan gada daga iyaye da kakanni.
Saurari shirin:
Your browser doesn’t support HTML5