AREWA A YAU: Muhimmancin Kafa Tashoshin Sauke Hajar Teku A Arewacin Najeriya, Fabrairu 01, 2023

Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

A cikin shirin na wannan makon, mun duba muhimmancin kafa tasoshn sauke hajar teku a tudu a yankin Arewacin Najeriya da ba ya kusa da gabar teku.

ABUJA, NIGERIA - Wadannan tasoshin sun fara zama zahiri daga kaddamar da ta Kaduna, sai kuma kammala aikin ta Funtua a Katsina da kuma yanzu an samu kaddamar da ta Kano a yankin Kumbotso.

A ziyarar sa a Kano a makon nan, shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci tashar da za ta zama hanyar bunkasa shigo da kaya da fitar da su ketare ba tare da dogon tafiya har zuwa Lagos ba.

Shugaba Buhari

Akwai bukatar kafa tashoshin a duk cibiyoyin kasuwanci na Arewacin Najeriya da hada tashoshin da layin dogo ko titin jirgin kasa.

Shiga shafin a saurari cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU: Muhimmancin Kafa Tashoshin Sauke Hajar Teku A Arewacin Najeriya, Fabrairu 01, 2023.mp3