AREWA A YAU: Bincike Kan Harin Rundunar Soja Kan Masu Maulidi A Igabi - Disamba 6, 2023

Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Fadar Aso Rock ta ba da tabbacin cewa shugaba Bola Tinubu zai tabbatar da an hukunta duk wanda a ka samu da sakaci har a ka samu yanayin mai ban takaici da tausayi.

Sabon shirin Arewa A Yau zai duba bukatar yin bincike kan harin da rundunar soja ta kai da jirgi marar matuki inda akasin ya fada wa masu Maulidi a Tudun Biri da ke yankin Igabi a jihar Kaduna.

Rundunar nan dai da ke aikin yaki da barayin daji a yankin arewa maso yamma ta bayyana cewa kuskure a ka samu lamarin ya shafi wadanda ba su da laifi.

Fadar Aso Rock ta ba da tabbacin cewa shugaba Bola Tinubu zai tabbatar da an hukunta duk wanda a ka samu da sakaci har a ka samu yanayin mai ban takaici da tausayi.

Kungiyar Ansarul Din Attijjaniyya da ke zama babbar kungiyar 'yan Tijjaniyya da ke gudanar da bukin Maulidi ta bukaci kaddamar da bincike na hakika da biyan diyya.

Da ya ke magana a madadin jagoran kungiyar, Khalifa Sanusi Lamido Sanusi, sakataren kungiyar Alkassim Yahaya ya karfafa fatan daukar matakan da su ka dace na bin kadun wadanda akasin ya shafa.

Da ya ke magana mai taimaka wa shugaba Tinubu kan labaru Abdul'aziz Abdul'aziz ya ce shugaban ya nuna damuwa ainun kan asarar rayukan.

Saurari shririn:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU