AREWA A YAU: Batun Kafa Wata Gidauniya Ta Tara Gudummuwa Don Inganta Tsaro A Sokoto - Nuwamba 1, 2023

Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Sabon shirin Arewa A Yau zai leka gabashin jihar Sokoto inda a dalilin kalubalen tsaro aka kaddamar da wata gidauniya don tara gudunmawa da za a yi amfani da ita wajen inganta tsaro a yankin.

Bayan kammala tara kudin, wanda har tsohon gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya ba da ta sa gudummuwar, an samu sabanin fahimta tsakanin dan majalisar dokokin jihar da asusun da ke karkashin tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa.

Dan majalisa da ke wakiltar yankin Aminu Almustapha Boza, na ganin ana tafiyar hawainiya wajen kashe kudin ga muradin da a ka saka a gaba. Bayanan sa sun sa wasu nuna cewa ya yi riga Malam masallaci ko kuma bai fahimci yadda lamarin ya ke ba.

Saurari shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU