Hatsaniyar da ta samo asali a daren jiya Laraba ta cigaba har zuwa wayewar garin Alhamis a yayin da bangarorin bata-garin 2 ke kokarin daukar fansa game da wani al’amari da ba’a bayyana ba.
A yayin hatsaniyar ne bata-garin suka cinnawa wasu shaguna makare da kayan abinci wuta.
Tuni dai aka tura ayarin farko na masu kai dauki da suka hada da jami’an ‘yan sanda dana kwana-kwana zuwa wajen da al’amarin ya faru.
Sai dai a cikin wata sanarwa, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, yace zaman lafiya ya dawo a kasuwar.
Yace “An kama fiye da mutane 50 da ake zargi da hannu a lamarin sannan an lalata gidajen wucin gadin da suke zaune a ciki, don haka an tarwatsa su yadda ya dace”.
“Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Legas, Adegoke Fayoade, ya bada umarnin gaggauta gurfanar da bata-garin gaban kotu, sannan yayi gargadin cewar rundunar za ta sanya kafar wando daya da duk wanda aka samu yana kokarin tada zaune tsaye, kamar yadda doka ta tanadar”, a cewarsa.