Kimanin shekaru bakwai kenan da ake ta takaddama tsakanin kamfanin Apple da Samsung, wanda kamfanin Apple ke tuhumar na Samsung da satar fasahar wayar shi, wanda rigimar har ta kai kotu anata shari.
Ya zuwa yanzu dai babu wasni sakamakon hukuncin da kotu ta yanke, duk dai da cewar a watan Mayu da ya gabata kamfanin na Samsung ya biya abokin hurdar shi Apple adadin dallar Amurka milliyan $399M, biyo bayan hukuncin kotu da ta bukaci kamfanin Samsung da ya biya Apple dalar Amurka milliyan $539M.
Idan har hukuncin na kotu ya zamana cewar Samsung zai biya Apple makudan kudaden, to ya zamana cewar Samsung zai karama Apple kimanin dallar Amurka milliyan $140M. Mai magana da yawun kamfanin Apple yaki bayyana sakamakon shari’ar.
Ya bayyanar da cewar “kamfanin yafi damuwa da matsalar satar fasaha, domin kuwa wannan matsalar tafi maganar kudi.” An kiyasata cewar kamfanin na Apple shine kamfanin da yafi shahara a duniya wajen kera wayoyin zamani, kudin da kamfanin zai karba ba wani abu bane gareshi domin yafi karfin kudin.