APC Taki Amincewa da Maganar Dage Zabe

Akwatunan zabe

Jam'iyyar APC ta fito fili taki amincewa da maganar dage zabe

Kin amincewar APC da batun dage zaben martani ne ta mayarwa jam'iyyu goma sha shida da suka kira sai a daga zaben wai, domin a samu a baiwa kowa katin zabe na din-din-din.

Su jam'iyyun sun fitar da wata takarda da suka sawa hannu suna kiran a dage zaben wai sai an samu katin din-din-din tukuna kafin a cigaba da yin zaben.

Sakataren jam'iyyar APC na kasa Maima La Boni yace sun yadda da shirin da hukumar zabe tayi kuma shugaban hukumar ya tabbatarwa kasa cewa ashirye suke su gudanar da zaben. Jam'iyyar ta kuma jawo hankulan dattawan kasa da zasu halarci taron kasa yau su yi hattara domin kada su jefa kasar cikin rudani.

Duk da irin wadannan kiraye-kirayen 'yan siyasa na cigaba da fafitikar neman zabe kana kungiyoyi dake zaman kansu suna cigaba da wayar da kawunan mutane akan zaben tare da yin anfani da kafofin labarai inda suke kiran 'yan kasa akan yunkurin dage zaben.

Wata kungiyar mata da ake kira WRAPA tace ta tabbata 'yan Najeriya suna son a yi zaben kuma kasar ta kashe kudi da yawa akansa, 'yan siyasa kuma suna nan suna fafitika sabili da haka babu wani dalilin da zai sa a dage zaben.

To saidai mai magana da yawun PDP Femi Fani-Kayode yace shawarar yi ko dage zabe ta hukumar zabe ce bata shugaban kasa ba ko PDP. Hurumi ne na hukumar zabe.

Ga rahoton Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

APC Taki Amincewa da Maganar Dage Zabe - 2' 38"