APC ta Zargi PDP da Shirin Yin Magudi a Zaben 2015

APC

Yayin da zaben 2015 ke dada karayowa manyan jam'iyyun siyasar Najeriya sun soma zargin juna
Jam'iyyar adawa ata APC ta zargi jam'iyyar PDP da shirin yin magudi a zaben shekara mai zuwa.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa Chief Bisi Akande ya zargi jam'iyyar PDP da cewa tana shirin tafka magudi a zaben 2015 da dabara ta hanyar bada cin hanci da tsoratar da wasu shugabannin cibiyoyin gwamnati masu zaman kansu. Chief Bisi Akande ya yi zargin ne a Ibadan lokacin taron gwamnonin APC jiya Litinin.

Shugaban APC yace sun taru ne domin nemo hanyar yin juyin juya hali ba tare da yin tarzoma ba ko zubar da jini.

Shi kuma mataimakin gwamnan jihar Boron Alhaji Zanna Mustapha yace idan sojojin Najeriya nada isasshen kayan aiki to su kama 'yan kungiyar Boko Haram. Domin idan gaskiya ne suna da makamai da suka fi na Boko Haram babu yadda 'yan kungiyar zasu dinga shiga koina a kowane lokaci su kashe mutane su yi kone-kone su kuma fita lafiya. Kuma an ce ba'a sansu ba. Wannan ba magana bace. Babu wanda bai sansu ba. Da a cikin mutane suke amma da aka matsa masu sun koma daji. Saidai abun takaici shi ne za'a yi tafiyar kusan kilomita dubu biyu kefen dajin da suka ja daga ba za'a ga sojoji dubu daya ba.

Dangane da jita-jitar cewa ana son a kafa kantoman soja a jihar ta Borno mataimakin gwamnan yace maganar banza ce. Ba'a irin wannan maganar cikin dimokradiya. Yace akwai yadda ake dakatar da gwamna. Amma ya kara da cewa su da suke karkashin dokar ta baci basu ba ne gwamnati. Sojoji su ne gwamnati. Mataimakin gwamnan yace su kawai suna kallonsu ne.

Your browser doesn’t support HTML5

APC ta Zargi PDP da Shirin Yin Magudi a Zaben 2015-3:48