Alhaji Bulama mai magana da yawun dattawan jihar Borno ya zanta da wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda dangane da lamarin. Yace dattawan jihar fiye da talatin sun yi taro kan maganar da suka ji na shirin cire gwamnansu. Yace suna mika sako ga shugaban kasa a kan yunkurin da yake so yayi wato na cire gwamnansu ya kuma kawo soja ya yi mulki.
A ganinsu bai kamata a yiwa gwamnansu Kashim Shettima wannan ba domin bashi da iko a kan sojoji ko 'yansanda. Yace sojoji aikinsu daban wadan da jama'a suka zaba kuma aikinsu daban. Sabo da haka abun da shugaban kasa yake niyar yi ba daidai ba ne. Dokar kasa bata bashi iko ba kuma bashi da hujjar yin hakan.
Dangane da cewa yakamata su bar batun ganin cewa fadar shugaban kasa ta fito da bayyana cewa bata san da wannan maganar ba kuma babu wani tunanin cire gwamnan sai wakilin dattawan yace "wanda maciji ya sareshi idan ya ga doguwar igiya sai ya ji tsoro" Yace akwai maganar gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi fadar ta sha cewa ba za'a cireshi ba amma kwatsam sai aka tsigeshi. A baya ma hakan ta faru. Yace suna ganin take-taken da ake yi idan suka yi shiru zasu wayi gari su ji cewa an cire gwamnan Borno. Saboda haka yanzu sun yi kuka duniya ta ji.
Kan hare-haren da jihar ke fama da su dattawan sun ce gwamnan bashi da labari yana ji ne a kafar labarai kamar yadda kowa ke ji.
Daga bisani dattawan sun ce idan har shugaban kasa ya yi gaban kansa ya aiwatar da cire gwamnan zasu tafi kotu. Idan ma ta kama su je har kotun koli a shirye suke.