ABUJA, NIGERIA - A alamun da ke nuna jam'iyyar da ke karagar mulki a Najeriya ta fara shirya babban taron ta a 26 ga watan nan shi ne fitar da wannan sanarwa da ta biyo bayan raba mukamai ga shiyyoyi inda yankin arewa ta tsakiya zai samar da sabon shugaban jam'iyyar.
Dukkan manyan 'yan takarar a shiyyar masu hannu da shuni ne da su ka hada da tsoffin gwamnoni da dan majalisar dattawa Sanata Sani Musa da ke cewa ya shirya a shata dagar zaben. Musa na martani ne kan raderadin tsayar da Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban.
Muhammad Sa'idu Etsu shi ne mafi karancin shekaru a 'yan takarar; ya ce shi ma a shirye ya ke wajen samo kudin fom din.
A na sa bangaren mai neman takarar shugaban matasa Abdullahi Sidi Ali da tsarin shiyya ya sa ya koma neman mataimakin shugaban matasan, ya koka cewa an zumbula kudi.
Ya zama abu mai muhimmanci jam'iyyar ta kawar da umurnin kotu na dakatar da babban taron da kuma rage tsamar gwamnoni matukar taron zai yiwu kuma ba zai bar baya da kura ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5