APC Ta Kammala Shirin Zaben Fidda Gwani Da Dukkan ‘Yan Takara

  • Saleh Shehu Ashaka

Taron jam'iyyar APC

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shirya gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa da dukkan ‘yan takara, bayan musanta cewa an fidda wasu daga cikin ‘yan takarar 23.

Shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu ya ce sun karbi kofin kwamitin tantance ‘yan takara kuma ba a cire sunan kowa daga cikin ‘yan takarar ba.

A hirar shi da Muryar Amurka, masanin harkokin siyasa na jami’ar Abuja Dr. Abubakar ya yi sharhi kan dage lokacin da APC ta yi don sanin dan takarar da PDP za ta tsayar.

Bisa ga cewar shi, duk muhawarar na kan uban jam’iyyar Bola Tinubu ne wanda jam’iyyar ta nuna za ta ladabtar da shi don kalaman da ya furta kan shi ya yi sanadiyyar lashe zaben shugaba Buhari a 2015.

Take-taken jam’iyyar bai yi wa wasu daga ‘yan cibiyar kamfen ta shugaba Buhari BSO irin su Alhaji Muhammad Murtala dadi ba, don su na ganin fito na fito a wannan yanayi na da hatsari.

Masanin kimiyyar siyasar Dr.Kari ya ce ya zama mai muhimmanci APC ta yi takatsantsan da jigon ta Tinubu wajen yin zabe mai adalci a fidda gwanin.

An fara daukar tsauraran matakan tsaro a Abuja musamman hanyoyin tsakiyar gari da ke dosar filin EAGLE inda za a gudanar da zaben.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

APC Ta Kammala Shirin Zaben Fidda Gwani A Litinin Din Nan Da Dukkan ‘Yan Takara