APC A Jihar Niger Ta Damu Da Kasancewar Wasu 'Ya'yanta Cikin Wadanda Suka Balle

APC

Reshen jam'iyyar APC na jihar Niger ya nuna damuwarsa bisa kasancewar wasu 'ya'yanta biyu a cikin jerin sunayen wadanda suka balle suka bi Buba Galadima

A jihar Niger jam'iyyar APC ta nuna damuwa da kasancewar sunayen wasu 'ya'yanta dake rike da mukaman siyasa cikin jerin sunayen wadanda suka kafa sabuwar Reformed APC, da Buba Galadima ke shugabanta.

Shugaban jam'iyyar na jihar Niger Injiniya Muhammad Imam, ya ce ganin sunayen dan majalisar dattawa Sanata David Umaru, da dan majalisar wakilai Abubakar Lado Suleja, ya zo masu da mamaki. Saboda haka ya ce sun ba 'yan majalisun wa'adin nan da mako guda su bayyana matsayinsu ko kuma jam'iyyar a reshen Niger ta dauki mataki akansu.

Sakataren tsare tsare na APC a jihar Ismaila Modibbo ya yi karin haske akan lamarin. Matakin farko da aka basu shi ne su gaggauta karyata sanya sunayensu a cikin bangaren da ya balle. Idan basu karyata ba jam'iyya zata hukumtasu.

Duk kokarin jin ta bakin Sanata David Umaru ya ci tura, amma shi dan majalisar wakilai Abubakar Lado Suleja wanda ya ce yanzu haka yana ziyara a kasar India ya ki ya tabbatar ko karyata kasancewarsa cikin wanda suka balle wai sai ya dawo kasar.

A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari

Your browser doesn’t support HTML5

APC A Jihar Niger Ta Damu Da Kasancewar Wasu 'Ya'yanta Cikin Wadanda Suka Balle - 2' 49"