APC ta nuna matukar damuwa da zargin ana yin anfani da 'yan majalisa wajen cimma bukatun jam'iyyar PDP.
Chief Oyegun yace laifukan masu rike da kujerun siyasa basa fitowa fili sai sun bar jam'iyyar PDP idan kuma sun dawo jam'iyyar a yi anfani da soso da sabulu a wankesu fes a nuna cewa su ne gimshikan cigaban dimokradiya.
Taron da shugaban jam'iyyar APC John Oyegun ya jagoranta ya zargi PDP da cewa tamkar tana neman mayar da dimokradiya ne mulkin kama karya. Mai Ma'ala Boni sakataren jam'iyyar yace cusa sojoji cikin harakar siyasa ba zata haifar ma kasar da mai ido ba. Ba alheri ba ne ga dimokradiya. A sakar ma sojojin mara su yi aikinsu na tabbatar da tsaro a kasar. Har yanzu a wasu sassan kasar wasu basa iya zuwa gonakinsu ko makarantu. Amma maimakon a bar sojoji su tabbatar da tsaro an sasu cikin aikin siyasa.
Ma'ajin APC Bala Gwagwarwa na ganin PDP na daukan matakan neman dawama kan mulki ne. Yace bai dace ba 'yan majalisa su dinga karbar kudi suna aikata abun da ba daidai ba ne.
Nan take sakataren watsa labarai na PDP Olisa Metuh yayi watsi da zargin. Ya nuna cewa APC na neman tada fitina ne domin jama'a su yiwa shugaba Jonathan bori. Yunwar 'yan adawa na kwabar da dimokradiya ke sasu yin kalamun batanci har ma da kushe majalisa da take wata gimshiki ce da take tallafe da dimokradiya, kushe aikinta kuma babbar barazana ce ga dimokradiya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5