Tun tafiya bata yi nisa ba jam'iyyar adawa ta APC ta dare biyu a jihar Taraba.
WASHINGTON, DC —
A jihar Taraba jam'iyyar adawa ta APC ta dare biyu tun kafin su kai koina.
Tuni bangarorin biyu suka bude ofisoshinsu kowanensu kuma na ikirarin shi ne halattacen shugaba. Batun ya raba kawunan 'yan jam'iyyar dake jihar. Akwai APC Sat bangaren wadanda kwanan nan suka shiga. Kana akwai APC na asali da ake kira "Mu a aka tarar"
A taron da su 'yan bangaren Sat suka yi a Jalingo sun zabi shugabannin jam'iyyar a karkashin jagorancin Alhaji Hassan Jika Ardo. Kamar yadda ya bayyana sun zo ne domin su kawo gyara. Ya ce kafin su yi zaben an bar komi kara zube babu inda 'yan jam'iyya zasu je su kai koke dalili ke nan ya ruga kotu inda ya sami hukuncin cewa yakamata a samu shugabanni na riko. Shugabannin da suke dasu a Abuja basu taba zuwa sun tambayesu ba menene suke ciki.
To saidai 'yan bangaren "Mu aka tarar a jam'iyya" sun ce zaben da 'yan sat suka yi ba zai karbu ba. Abdullahi Tulu tsohon sakataren ANPP jigo a jam'iyyar ya ce abun da ya faru wasu tsiraru ne suka zauna suka yi. Suna ganin idan an yi zabe ba zasu sami madafa ba. Ya ce su ne suka kebe kansu suka shirya zaben bogi.
Alhaji Umaru Tuhu mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa mai kula da jihohin arewa maso gabas ya ce wanda suka yi zabe sun ce sun yi ne domin bai kamata a bar mutane kara zube ba. Amma sun amince duk ran da ya zo jihar ya shirya zabe zasu bi abun da ya yi ba wai lallai sai zaben da su suka yi ba.
Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5