Kakakin babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya APC Lai Muhammed yace ganin Modu Sheriff da Shugaba Jonathan a kasar Chadi ya nuna abubuwa uku.
Na farko Modu Sheriff ya fi karfin a yi masa bincike. Alakarsa da shugaban kasa kuma ta if tsaron kasar mahimmanci. Alakar shugaba Jonathan da Modu Sheriff tamkar ta karya matsayinsa na shugabanci ne. Yanzu zargin da jam'iyyar keyi na cewa PDP na anfana da Boko Haram ya zama gaskiya.
Jigon APC Faruk Adamu Aliyu ya bukaci kotun duniya ta binciki shugaba Jonathan. Idan har kasar Amurka zata sa a kama shugaban kasar Sudan Al-Bashir da kuma hana Mugabe yawo a duniya saboda ana zarginsu da cutar dan Adam to hakikan shugaba Jonathan ya cancanta shi ma kotun duniya ta gurfanar dashi.
PDP tayi watsi da zargin tana cewa shafi fadin 'yan siyasa ne. Tsohon kwamishanan labarun jihar Borno Ino Bola yayi watsi da zargin da cewa Ali Modu Sheriff na kasuwancinsa ne a Chadi. Sam baya cikin tawagar shugaba Jonathan. Shugaba Jonathan ya samu Modu Sheriff ne a Chadi inda shi ne shugaban 'yan Najeriya a kasar. Sabili da haka babu yadda shugaban kasa zai kai ziyara Chadi Modu Sheriff ya kasa kasancewa a wurin tarbarsa ba. Sun nuna hoton da suke gaida shugaban Chdi amma basu nuna hoton da Modu Sheriff da 'yan Najeriya suke tarbar shugaban Najeriya ba.
Zargin na 'yan siyasa ne inda suke juya magana ta yadda suke so. Bisa ga gaskiya mai magana da yawun Modu Sheriff yace bai tafi Chadi a tawagar shugaban Najerya ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5