APC Reshen Jihar Bauchi Ta Dakatar da Wani Dan Majalisar Wakilai

APC

Jam'iyyar APC reshen jihar Bauchi ta zargi Ahmed Yerima dan majalisar wakilan Najeriya da karya dokarta ta hanyar furta wasu kalamai da basu kamata ba a bainar jama'a

Kakakin jam'iyyar na jihar Bauchi Alhaji Awal Jalla ya shaidawa Muryar Amurka cewa kada wani dan jam'iyyar zababbe ko ba zabbabe ba ya ci mutuncin dan'uwansa dan jam'iyya, kada kuma ya fitar da maganar cikin gida waje.

Alhaji Jalla yace babu dan jam'iyyar da ya shigota da bai amince da dokokinta ba. Yace Yarima Abdullahi ya yadda da dokokin jam'iyyar kafin ya sa hannun amincewa. Yace basu dakatar dashi akan gaskiyar da yake da ita yana fada ba. Idan yana da abubuwan da zai fada ya san ofishin jam'iyyar kuma can ya kamata ya je ya fadi albarkacin bakinsa. Alhaji Jalla yace tunda aka zabesh idan majalisa bai taba zuwa ofis da wani korafi ba ko kuma rubuta wasika wa jam'iyyar.

To saidai Malam Ahmed Yarima wanda aka dakatar yace shi bai karya wata doka ba illa dai ya bayyana ra'ayinsa akan yadda abubuwa ke gudana a jihar Bauchi. Yace abun da jam'iyyar ta yi masa bashi da tushe domin sai mutum ya aikata laifi kafin a dakatar dashi ko a koreshi. Na biyu yace kafin a dakatar da mutum sai an ji ba'asinsa. Yace illa iyaka 'yan Buharin lafiya ne, 'yan neman gindin zama su ne suka tsaya dole dole sai an dakatar dashi daga jam'iyyar.

Yarima ya kara da cewa babu wata doka da ya karya illa iyaka ya bayyana bukatun al'umma. Yace ya kare mutunci al'umma kuma ya bi kadunsu. Yace abu ne a bayyane. Dubun dubatan mutane sun fito sun yi zanga zanga kan rashin biyansu albashi. Ke nan dan mutum ya fito ya yi magana sai a koreshi. Yace ai jam'iyya ba ita ce Allah ba.

Sabo Muhammad mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi a fannin labaru yace babu ruwan gwamnati da abun dake faruwa tsakanin jam'iyyar da Ahmed Yarima.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

APC Reshen Jihar Bauchi Ta Dakatar da Wani Dan Majalisar Wakilai - 2' 54"