Rundunar ‘yan sanda jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce, jam’iyyun APC da NNPP sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a jihar gabanin hukuncin da kotun daukaka kara za ta yanke kan zaben gwamna a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a jawabi da ya yi wa manema labarai wanda Kakakin ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.
Kwamishina Gumel ya ce hukumomin tsaron jihar za su hukunta duk wanda ya yi yunkurin ta da husuma gabani ko bayan sanar da hukuncin da kotun daukaka karar za ta yanke a Abuja, babban birnin Najeriya.
A ranar Juma’a kotun daukaka kara a Abuja, babban birnin Najeriya za ta yanke hukunci kan karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya daukaka a kotun.
Gwamna Yusuf na kalubalantar hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben gwamna a jihar ta yanke a ranar 20 ga watan Satumba inda ta rushe nasararsa ta ayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a watan Maris din 2023.
Kotun sauraren kararrakin zaben karkashin Alkalai uku da suka samu jagorancin Justice Oluyemi Akintan Osadebay, ta rage wa Yusuf kuri’u 165, 663 saboda babu sa hannu da tambarin hukumar zabe ta INEC.
Hakan ya sa kuri’un da ya samu a zaben suka koma 853, 939 yayin da na Gawuna suka ci gaba da zama a matsayin 890, 705, wanda ya hakan ya sa kotun ta ayyana Gawuna a matsayin asalin wanda ya lashe zaben.
Sai dai Yusuf ya garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar wannan hukunci yana mai cewa ba a yi masa adalci ba.
Yayin da wasu ke nuna fargabar barkewar rikici a jihar, tuni rundunar ‘yan sandan ta ce ta dauki kwarara matakai ciki har da sa shugabannin jam’iyyun siyasan biyu su rattaba hannu kan yarjejeniayar tabbatar da zaman lafiya a Kano.
“Muna masu ba ku tabbacin cewa, shugabannin jam’iyyun siyasan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ofishin Kwamishinan ‘yan sanda.” In ji Kwamishinan ‘yan sanda Gumel.
Ga batutuwan da aka cimma karkashin yarjejeniyar da shugabannin jam’iyyun NNPP da APC suka rattaba hannu a kai:
- Ba za a bar wata jam’iyya ta yi taron mutane a kowanne yanki na jihar Kano ba.
- Dukkan magoya bayan jam’iyyun ba za su yi wani taro na gayya don yin zanga-zanga ko bore ko yin murna ba, domin kada hakan ya janyo wata matsala.
- Za su wakilici jam’iyyunsu wajen sa ido tare da ganin an aiwatar da dukkan sharuddan da aka cimma karkashin yajejeniyar a gaban kwamishinan ‘yan sanda.
- Dukkan jam’iyyun za su marawa hukomomin tsaro baya wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya karkashin matakan da hukumomin tsaro suka dauka.
- Duk wanda aka samu da laifin ta da tarzoma a lokacin hukuncin ko bayan hukuncin da kotun daukaka karar za ta yanke zai fuskanci fushin hukuma.