Rashin jituwa tsakanin gwamna Godwin Obaseki, da shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomohle na kara ta’azara, inda reshen jam’iyyar na jihar suka dakatar da Oshiomohle.
Gwamnan yace ba Oshiomhle ne ya dora shi a kan kujera ba, mutane ne suka bada gudunmawa wajen zaman sa gwamna a jihar ta Edo, inda ya karbi mulki daga Oshiomohle bayan kammala wa’adin sa na biyu.
Masu zargin Oshiomohle da mulkin kama karya a APC irin su jigon jam'iyyar a jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura yace tuni ya dace a dakatar da Oshiomohle..
Sakataren walwala na APC Ibrahim Masari, wanda ke cewa jam'iyyar ta dau mataki saboda kawo karshen takaddamar da sulhunta bangarorin biyu da ke hamayya da juna.
Masana siyasa na ganin yana iya yiwuwa, jam’iyyar ta kasa ta kori shugabannin jam’iyyar na jihar Edo.
Ga rahoto cikin sauti daga wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5