Kwanaki 9 ke nan, ana ta kai ruwa rana, tare da dage zaben na fitar da ‘yan takara ana sake shata lokaci har fiye da sau 4, kazalika da sauya ‘yan kwamitin gudanar da zaben daga uwar jam’iyyar ta kasa, daga karshe dai zaben bai yiwu ba, har ya zuwa karfe sha biyun daren jiya, wa’adin da hukumar zabe ta baiwa jam’iyyu na gabatar da ‘yan takararsu.
Sabon kwamitin zaben wanda ya isa garin Gusau tun a ranar Asabar, ya kwashe tsawon kwanaki biyu yana ganawa da ‘yan takara 9 da ke neman tsayawa takarar gwamna, da kuma sauran ‘yan takarar Majalisun tarayya da na jiha, tare zimmar yin sulhu, to amma lamarin ya juye zuwa rigima har ma da baiwa hammata iska.
To sai dai duk da yake ‘yan kwamitin zaben tare da kayan aikin zaben basu ko bar otal din da suke ba, a daren jiyan, gwamnan jihar ta Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar, ya shugabanci wani zama a ofishin jam’iyyar na jiha, a inda aka ce an bayyana sakamakon zaben fitar da gwani, inda aka bayyana Muktar Shehu Idris mai goyon bayan gwamna Yari, a zaman wanda ya lashe zaben fitar da gwani na gwamna.
To amma a bangare daya, kwamitin da uwar jam’iyyar ta aiko domin gudanar da zaben, ya tabbatar da cewa ba’a yi zaben ba saboda wasu dalilai.
Yanzu haka dai jama’ar jihar ta Zamfara musamman ‘ya’yan jam’iyyar APC, sun kasa kunne domin jin yadda zata kaya a wannan lamari, a daidai lokacin da ake ganin jam’iyyar na fuskantar barazanar rasa ‘yan takara a jihar, a babban zabe na shekara ta 2019 mai zuwa.
Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5