Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Dan Takarar Gwamna A Adamawa Ya Wuce Ya Bar Baya Da Kura


ADAMAWA: Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo
ADAMAWA: Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Bayan tirka tirkan da aka ta yi yanzu haka an kammala zaben fidda gwani na jam’iyar APC na gwamna a jihar Adamawa, Gwamnan Jihar Sanata Muhammadu Bindo Jibrilla, ya lashe zaben inda sauran yan takara suka garzaya Abuja domin mika kukansu.

Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na takarar kujerar gwamna na jam’iyar APC ke nan na jihar Adamawa Manjo Janar Ahmad Tijjani Jibrin, ke bayyana gwamnan jihar Sanata Muhammadu Bindo Jibrilla, da cewa shi ya lashe zaben fidda gwani.

To sai dai yayin da bangaren gwamnan jihar ke murna, su kuwa 'yan takarar da suka tsaya takara da gwamnan jihar suka garzaya shelkwatar jam’iyar a Abuja, domin mika kukansu game da yadda aka gudanar da zaben.

Dr Mahmud Halilu Ahmad, dake zama kanin matar shugaban kasa Aisha Buhari, yace ba zata sabu ba, wai bindiga a ruwa.

A gangamin da magoya bayan Bindo suka shirya, gwamnan jihar yace zai hada kawunan 'ya'yan jam’iyar domin samun nasara a babban zaben dake tafe.

Zaben Dan Takarar Gwamna A Adamawa Ya Wuce Ya Bar Baya Da Kura 2'50"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG