Wannan buki ya samu hallartar shuwagabannin jam’iyyun siyasa na kasar.
Da yake rantsar da ita, shugaban kasa John Dramani Mahama ya ambato gogewa da tayi a fanni daban-daban inda ya kyautata mata zaton yin wannan aikin.
Sai dai shugaban ya tunatar da Mrs. Osei yace wannan babban aiki ne, da aka dora miki, don haka ya zama wajibi kiyi aiki tukuru kamar yadda jama’ar kasar suke hasashe.
Shugaba Mahama ya cigaba da yin bayani inda ya yabawa tsohon shugaban hukumar zabe mai barin gado yana cewa “Dr. Kuji Afarajad ya tabbatar wa kasar nan gogewarsa tsakanin shekaru 20 wajen tsara shirye-shiryen zabe da gudanar da zaben. Ya ce duk da irin korafi da muke a matsayin mu na ‘yan siyasa, a cikin gwamnati ko ‘yan hamayya”.
A nata bangare, sabuwar shugabar hukumar Mrs. Osei tayi alkawari tana cewa “da gudunmuwar sauran ma’aikata na hukumar zata yi kokari ta cigaba da karfafa hukumar domin ta iya yin aiki babu sani, babu sabo.”
Kafin wannan mukami Charlotte itace shugabar hukumar wayar da al-ummar kasa akan hakkokinsu da wajibobinsu ga kasar.
Your browser doesn’t support HTML5