Wata hayaniya ta barke a majalisar dokokin Najeriya a yau dinnan, Yayinda jami’an tsaro suka yi kokarin hana kakakin majalisar wakilan kasar shiga ginin majalisar.
‘Yan sanda sun gaya ma muryar Amurka cewa sun harba barkonon tsohuwa a lokacin da hayaniyar ta tashi tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan Kakakin Majalisar Aminu Tambuwal kusan su 200.
Kakakin majalisar ya canza sheka daga jam’iyyar PDP mai mulki, zuwa babbar jam’iyyar adawa ta APC, abinda yake ci gaba da harzuka ‘yan jam;iyyar PDP.
Jaridun kasar sun ruwaito cewa ‘yan sandan ciki da yawa ne suka mamaye ginin majalisar tun kafin a fara taron, wanda da Kakakin Majalisar Aminu Tambuwal ne zai jagoranta.
Rahotanni sun fadi cewa da farko ma an hana kakakin majalisar shiga ginin amma wasu ‘yan majalisar suka sa baki, suka bata kofar shiga ginin da ga nan suka samu suka shigar da shi kakakin majalisar.
Ana sa ran majalisun za su tattauna bukartar gwamnati ta tsawaita dokar ta-bachi a jihohin arewa maso gabashin kasar guda 3, inda sojojin Najeriya ke fafatawa da ‘yan kungiyar masu tsattauran ra’ayi da ake kira Boko Haram.
zaman da aka soke yau, da shine zai zama karo na farko da kakakin majalisar zai je tun bayan da ya canza sheka.
Ana sa ran jami’iyyar adawa ta APC ce zata zama babban kalubale ga jam’iyya mai mulki da kuma shugaba Jonathan a zaben watan fabairun da za a yi a shekara mai zuwa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5