Wadansu Mutane da aka kebe a cibiyar kula da wadanda suka kamu da cutar coronavirus a jihar Naija, sun gudanar da bore saboda nuna rashin gamsuwa da yadda ake kula dasu a cibiyar.
Kafofin Sadarwa na zamani sun yi ta yayata wannan boren, al’amarin da gwamnatin jihar ta ce tana sane da shi. Sakataren gwamnatin jihar ta Naija kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana cewa ya kamata mutane sun gane idan an kebe mutum, to an yi ne domin kare lafiyarsa da kuma ta sauran al’umma.
A Najeriya dai wannan shine karo na biya da aka sami irin wannan boren a irin wadannan cibiyoyi, al’amarin da Masu Sharhi ke ganin abin dubawa ne.
Masani a harkar kiwon lafiya kuma Babban Sakataren kungiyar ba da agajin musulunci a Najeriya, Dr. Abba Yahaya ya ce, karancin kulawa ne ke sanya irin wannan tarzomar a irin wadannan cibiyoyi, saboda haka akwai bukatar hukumomi su kara inganta matakan kula, amma ya ce, ya kamata su kuma al’umma su gane yin boren ba shine mafita ba.
Sakataren gwamnatin jihar Nijer, Ibrahim Matane ya ce, zama a irin wadannan wurare sai da hakuri. Saboda haka ya ce jama’a su kara hakuri.
Ya zuwa yanzu an sami karin mutum biyu masu dauke da cutar coronavirus a jihar Naija, hakan ya kawo jumlar mutane biyar ke nan da su ka kamu da cutar a jihar. Haka zalika a hau Al’hamis, za a sallami wasu Al’majirai 26 da aka dawo dasu daga jihar Kaduna aka puma kill ace su makonni biyu da suka gabata a sakamakon rashin samun su da cutar.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5