Anya Kuwa Amurkawa Sun Shirya Zaben Mace Shugaba?

Sanata. Kirsten Gillibrand

'Yar majalisar dattawar Amurka Sanata Kirsten Gillibrand, ta bayyana aniyarta na tsayawa takarar shugabancin Amurka a zaben shugaban kasai mai zuwa.Tana cikin jerin mata dake neman wannan matsayi karkashin jam'iyyar Demockrat.

A jiya Lahadi ta ayyana nufin nata, wanda zata gabatar da jawabin ta na farko a sati mai zuwa a gaban Otel din Trump International dake birnin New York. Tace Amurka na bukatar jagora mara tsoro, mai nagarta, wanda kuma bai da tsoron kawo canji ta kowane hali.

Malam Mohammed Nasiru, malami a jami'ar birnin New York, yayi sharhi akan rawar da mata zasu taka a siyasar Amurka a zabe mai zuwa. wanda yake ganin cewar da sauran lokaci ace mata su shugabanci kasa irin Amurka.

Yana ganin cewar Amurkawa basu shirya zaben macce ta ja ragamar mulkin su ba, idan aka yi la'akari da irin zaben da ya gabata, yadda Hillary Clintor tayi kamfe da kuma irin rawar da ta taka a siyar Amurka, ana iya cewa ita zata ci zaben amma daga baya sai ga akasion hakan.

Malam. Nasihu, na ganin cewar kamar da sauran lokaci kamin mata su fara taka gaggarumar rawa a siyar Amurka, kamun kuma ace sauran kasashe a fadin duniya su dauka.

Baba Yakubu Makeri ya tattauna da shi ga kuma yadda firar ta kasance.

Your browser doesn’t support HTML5

Anya Kuwa Amurkawa Sun Shirya Zaben Mace Shugaba? 2'30"