Angola Ta Fitar Da Morocco A Gasar BAL, Ta Kai Semi-final

Dan wasan Angola, Carlos Morais a lokacin gasar ta BAL

Wannan nasara na nufin, ‘yan wasan na Angola sun kai zagayen Semi-finals, yayin da Morocco ta fice a gasar ta BAL.

Kungiyar ‘yan wasan kwallon Kwando Atltico Petroleos ta kasar Angola, ta lallasa Association Sportive de Sal ta kasar Morocco da ci 79-72, a wasan Quarter-final na gasar zakarun kwallon Kwando ta BAL da ake yi Kigali na kasar Rwanda

Dan wasan Angola Gerson Gonclaves ya zura kwallayen da suka ba kungiyarsa maki 19, ya kuma mayar da kwallaye 10 kana ya taimaka an zura guda shida.

Kazalika, Carlos Morais da Leonel Paulo, dukkan su sun kara maki 17 a kwallayen da suka sha, wadanda suka kai su ga gaci.

Wannan nasara na nufin, ‘yan wasan na Angola sun kai zagayen Semi-finals a gasra ta BAL, yayin da Morocco ta fice a gasar.

An kirkiri wannan gasa ce da hadin gwiwar hukumar kwallon Kwandon Amurka ta NBA da kuma ta kwallon Kwando ta duniya.

Wannan shi ne karon farko da hukumar NBA ta kaddamar da wata gasa a wajen yankin arewacin Amurka. Ga jerin sunayen kungiyoyin da zakarun ‘yan wasansu da suka fi fice.