Ana Zargin Wani Soja Da Kashe Mai Sayar Da Kankana A Zamfara Saboda Ya Tambayi Kudinsa

Kankana

“Rundunar sojin Najeriya na nuna takaicinta bisa wannan abin alhini da ya faru, tare da mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan mamacin.”

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kaddamar da bincike dangane da rahotannin da ke nuna cewa wani sojanta ya bindige wani mai sayar kankana har lahira a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne bayan da sojan, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya sayi kankana a wajen mutumin amma ya ki biyansa kudinsa,

Bayanai sun yi nuni da cewa, da mai sayar da kankanar ya tambaye shi sai ya harbe shi lamarin da ya mkai mutuwar mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba.

“Rundunar sojin Najeriya na nuna takaicinta bisa wannan abin alhini da ya faru, tare da mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan mamacin.” Wata sanarwa da Kakakin sojojin Najeriya Brig. Mohammed Yerima ya fitar a ranar Talata ta ce.

Karin bayani akan: Manjo Janar Usman Yusuf, jihar Zamfara, Sokoto,Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“Yana da kyau jama’a su sani cewa, kwamandan dakarun runduna ta 8 da ke yankin, Manjo Janar Usman Yusuf, ya kafa kwamitin bincike don gano yadda lamarin ya kai ga rasa rai.”

Sanarwar ta Yerima ta kara da cewa, ana kokarin gano sojan da ya aikata wannan danyan aiki.

“Rundunar sojin Najeriya ba za ta lamunci dakarunta su rika aikata irin wannan danyan aiki akan mutanen da ya kamata a ce suna karewa ba.

“Da zaran mun gano shi, za a gudanar da bincike, kuma idan aka same shi da laifi, zai fusknaci fushin hukuma daidai da yadda doka ta tanada.” In ji Yerima.

Rahotannin sun ce bayan da sojan ya kashe mai sayar da kankanar, matasa sun yi kokarin abka masa amma ya tsere ya shiga wani otel da ke kan hanyar Gusau zuwa Sokoto.

Wasu rahotanni sun ce matasan sun huce fushinsu akan wata motar sojoji, inda suka kona ta kurmus.

Amma rundunar sojin ta Najeriya, ta musanta wannan ikirari.

“Yana da kyau mu fayyace cewa, babu wata motar soja da aka kona kamar yadda rahotanni ke cewa.”