A jihar Lagos da ke kudancin Najeriya, ana zargin sojojin ruwan da kwace ma wasu mutane katunan su na zabe yayin da a ke shirin gudanar da zabuka a ranar asabar mai zuwa.
Wakilin Muryar Amurka ya ruwaito cewa lamarin ya auku ne a yankin da ake kira Marine Base da ke Apapa a jihar ta Lagos.
Mafi yawan wadanda a ke kwacewa katunan na zabe kamar yadda wakilin Muryar Amurka ya ruwaito masu sana’ar acaba ne.
“Sun tare ne ni a yankin Marine Base, ya karbi makullin babur dina ya kuma yi biris da ni na wani tsawon lokaci, da na mai magana sai ya tambaye ni ko ina da katin zabe na ce mai ina da shi, sai ya karba.” In ji Mustapha Muhammed wani dan asalin jihar Borno da ke sana’ar acaban.
A cewar Muhammed, sojan ya kuma nemi ya bashi kudi baya ga katin zaben shi da ya karbe, lamarin da ya ce bai yi mai dadi ba.
Tuni dai wannan batu ya fara jan hankulan shugabannin al’umar Hausa mazauna yankin inda su ka koka da abin da ke faruwa.
“Gaskiya wannan abu abin bakin ciki ne a ce katin zabe wanda ‘yan cin ka ne na cikakken dan kasa a ce an karbe shi. Mun nemi mu san dalilin karbar wannan kati ba mu sani ba.” Alhaji Musa Shabiri, wani shugaban matasa a jihar ta Lagos ya ce.
A cewar Shabiri, wannan ba shi ne karon farko da ake samun wannan matsala ba, yana mai cewa lamarin ya faru a wurare da dama.
“Bamu san soja da haka ba har yanzu mun kasa gane menene dalilinsu.” Ya kara da cewa.
Kokarin jin ta baki rundunar sojin ruwan domin a ji me za su ce game da wannan zargi ya cutura a lokacin hada wannan rahoto.
A ranar asabar mai zuwa Najeriya ke shirin gudanar da zabukanta inda shugaba Goodluck Jonathan zai sake neman shugabancin kasar a karkahsin jami’yar PDP sannan Muhammadu Buhari zai kalubalance shi a karkashin jam’iyar APC mai adawa.
Your browser doesn’t support HTML5