Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce dangane da zargin cin zarafin wata mata da wani sanatan majalisar dokokin Najeriya ya yi, wacce wani hoton bidiyon ya nuna yana dukan ta, bidiyon da yanzu haka ya karade shafukan sada zumunta.
Jama'a da dama hade da kungiyoyin kare hakkin bil adama na ta kira ga Sanata Elsiha Abbo ya sauka daga mukaminsa bayan bullar wannan zargi na cin zarafi.
Lamarin ya faru ne a wani kantin sayar da robobin yin jima'i a Abuja kamar yadda bidiyon ya nuna.
A cikin bidiyon wanda na'urar daukan hoton shagon ta dauka, an nuna wani mutum yana wanka wa wata mata mari bayan kaurewar wata takaddama da ta taso.
Tuni dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta kaddamar da bincike kan wannan al'amari.
Wakilin Muryar Amurka a Adamawa, jihar da Sanatan ya fito, ya ruwaito cewa al'umar mazabar yankin da Abbo ya fito ta nuna damuwarta kan aukuwar wannan lamari.
Baya ga haka, ita ma jam’iyyarsa ta PDP, za ta gudanar da na ta binciken a cewar Sakatarenta Hon. Abdullahi Adamu Prembe.
Kungiyoyin kare hakkin bani adama irin su Centre for Human Rights Advocacy ta ce dole a binciki wannan zargi, inda shugabanta, Komared Gambo Daud, ya nuna takaicinsa bisa aukuwar wannan lamari.
Ga cikakken rahotun wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul-'Aziz daga Yola.
Your browser doesn’t support HTML5