Bam din ya tashi ne a gundumar Huriwaa dake arewacin babban birnin kasar Mogadishu, kusa da mararrabar Balad kuma ya lalata motar daukar ruwa.
Wasu shedun gani da ido sun fadawa sashen Somaliya na Muryar Amurka cewa bayan bam din ya tashi, sojojin zaman lafiya sun yi farautar wadanda suka kai harin, nan ne suka harbe wasu fararen hula guda hudu a wani shagon gyaran mota dake kusa da wurin. Wadanda aka kashen sun hada da wasu direbobin motocin jama’a da wani direban wata babbar mota da ta lalace.
Jami’an gwamnatin Somalia sun tabbatar da harin bam a kan ayarin sojojin da kuma mutuwar da ta biyo baya.
Shedun da iyalan wadanda aka kashen suna zargin sojojin wanzar da zaman lafiyar na Kungiyar Tarayyar Afrikan da kashe fararen hular bisa ganganci a matsayin martani. Mai Magana da yawun sojojin zaman lafiyar da ake kira AMISOM a Somalia, yace rundunar tana kokarin tattara bayanai a kan batun, sai dai ya kara da cewa bai tsammaci za a kashe wani farin hula da gangan ba.
Tuni mayakan sa kai na al-Shabab suka dauki alhakin kai harin bam na gefen hanya kuma suka ce harin ya kashe sosjojin Tarayyar Afrika.