Ana Zargin An Yi Facaka Da Kudaden Jama'a

Gudanar da bincike akan wadannan aiyuka na kawata birane na ( NIAMEY NYALA) ya zama wajibi, domin kudaden da aka gudanar da wadannan aikace aikace kudaden jama’a ne.

A jamhuriyar Nijar yayinda hukumar kawata birane ( NIAMEY NYALA) ta kaddamar da aiyukan tsaftace birnin yamai wasu jami’an kare hakkin jama’a sun bukaci a gudanar da bincike akan wasu alamomin da aka gina a magamar manyan santoci. Suna masu cewa an yi facaka da makuddan kudade yayinda talakkawa ke cikin halin kuncin rayuwa.

Miliyan dubu uku da dari tara na Saifa ne aka kiyasta cewa an kashe domin gina alamomin na magamar hanyoyi da zanmar bayar da kyakyawan fuska ga birnin Yamai, abinda ya haifar da ce ce ku ce a shafukan sada zumunta tsakanin masu suka da masu kare tsarin na “Niamey Nyala”.

Wani mai fafutuka hakkin jama’a, Abdu Idi na cewa gudanar da bincike akan wadannan aiyuka ya zama wajibi, domin a cewarsa kudaden da aka gudanar da wadannan aikace aikace kudaden jama’a ne yana mai cewa hankali baya iya dauka ace ayi wannan aiki akan fiye da miliyan dari hudu da hamsin (450).

Mai Magana da yawun hukumar kawata birnin na Yamai, Madam Mariya Isa Bube, tace yau idan aka ce za a tsayawa za ayi a saurari abinda mutane ke fadi ba za a samu ci gaba ba ta kara da cewa jita jitan mutane ne kawai na son bata tsarin da aka fito dashi na kawata birnin.

Tun baya sagaye da shugaban kasar Nijar, ya gudanar a manyan titunan yamai, hukumar “Niamey Nyala” ke shan suka daga jama’a, aiyukan dake bukatar gudumuwar jama’a, zargin rashin tabuka wani abin a zo a gani game da aiyukan kawar da datti daga titunan birnin Yamai, ya jawo wa ma’aikatar magaji gari soke soke daga mazauna wannan gari.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Zargin An Yi Facaka Da Kudaden Jama'a - 3'05"