Ana Zanga Zangar Wanke Dan Sanda Farar Fata Da Kotun Amurka Ta Yi

Mutanen da suke zaman dirshan kan wanke wani dan sanda farar fata da wata kotu ta yi bayan da aka tuhume shi da laifin kisan wani bakar fata a 2011 a Amurka

Ana zanga zanga a Amurka bayan da wata kotu ta wanke wani tsohon dan sanda farar fata daga zargin kisan wani bakar fata a St. Louis da ke jihar Missouri.

Masu zanga zanga sun yi tattaki a birnin St. Louis da ke jihar Missouri, bayan da wata kotu ta wanke wani tsohon dan sanda farar fata daga zargin kisan wani bakar fara mai shekaru 24.

An zargi Jason Stockley, wanda baya aiki tare da rundunar ‘yan sanda birnin ta St Louis a yanzu, da harbin Anthony Lamar Smith a kusa-da-kusa, bayan wani guje-gujen mota da suka yi a watan Disambar shekarar 2011.

Masu shigar da kara, sun kuma zargi Stockley da dasa bindiga a kusa da gawar Smith bayan da ya harbe shi.

Domin gujewa abinda ya faru a birnin Ferguson dake kusa da St. Louis a shekarar 2014, gwamnan jihar Missouri, Eric Greitens, ya sa jam’ian tsaro na musamman su zauna cikin shirin ko-ta-kwana.

Hakan ya sa a jiya Juma’a wuraren kasuwancin da dama suka rufe, suka sallami ma’aikatansu da wuri, sannan makarantu ma suka sallami dalibai da wuri.

Masu zanga zangar sun fara taruwa ne akan tituna, bayan an jima da yanke hukuncin da safiyar jiya Juma’a.