Ana Zaman Doya Da Manja Tsakanin Shugaba Trump Da Hukumomin Leken Asirin Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya dauki matakin maye gurbin babban jami’in leken asirin gwamnatinsa, bayan da wani jami’in leken asirin Amurka ya gargadi ‘yan majalisar dokokin kasar a makon da ya gabata, a cikin wani bayanin sirri cewa, Rasha tana sake yin katsalandan a zaben shugaban Amurka.

Jaridar Washington Post da ta New York Times sun ruwaito a jiya alhamis cewa, shugaban ya nuna rashin jin dadinsa bayan da ya sami labarin yin wannan takaitaccen bayanin, ya damu da cewa mai yiwuwa jami'an sun yi wani bayanai da za a iya amfani da su a kan shi.

Jaridar New York Times ta rawaito cewa, shugaban ya nuna bacin ransa kuma ya kadu ne sakamakon bayanan daya daga cikin manyan mataimakan Maguire, Shelby Pierson, wadda ta fadawa 'yan majalisa cewa, Rasha tana katsalandan a yakin neman zaben shugaban Amurka na shekarar 2020, tana kokari taga an sake zabar Trump.

Zaman doya da manja da ke tsakanin shugaba Trump da hukumomin leken asirin Amurka, ta fara ne tun a lokacin zaben shugaban kasa na shekarar 2016, lokacin da kungiyar leken asirin ta yanke hukunci, "Shugaban Rasha Vladimir Putin da gwamnatin Rasha sun himmatu ne don taimakawa zababben shugaban wajen ganin an zabi shugaba Trump ko ta halin kaka."