Ana Yiwa Mata Da Yara Fyade A Gidajen Yarin Maiduguri-Amnesty International

Amnesty International

Najeriya Kungiyar kare hakin dan adam ta Amnesty International ta fito da rahoto da ke nuna cewa ana yiwa mata da yara fyade a gidajen yarin gwamnati guda biyu a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno,amma hukumar kula da gidajen yarina kasa ta musanta zargin

A lokacinda yake yiwa manema labarai bayanin yadda aka samu rahoton, mai magana da yawun kungiyar Amnesty International, Isa Sanusi ya ce sun dauki lokaci suna bincike akan jan hanakali da wani fursuna mai sauna Charles Okah yayi,inda ya ce an hada mata da yara da manyan maza a wuri daya, ana kuma cin zarafin matan da yaran ta hanyar yi masu fyade,ya ce wannan abin tashin hankali ne ganin cewa galibin fursunonin wadanda ta'addancin Boko haram ya daidaita su ne. Ya kuma yi kira ga gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Kula da Gidajen yari Francis Enobore ya ce wanan zargi ne Kungiyar Amnesty ta yi domin bai zo daidai da binciken da suka yi ba, duk da cewa suna cigaba da bin gidajen yarin kasar suna bincike. Enobore ya ce gidajen yari da ke Maiduguri na cikin wadanda suke dubawa.

Abin jira a gani shi ne irin matakan da Ma'aikatar kula da gidajen yarin zata dauka wajen raba manya da mata da yara daga zama a wuri daya domin gudun wannan irin ta'asa da aka ce tana aukuwa a gidajen yarin.

Saurari cikakken rahoton Madina Dauda

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton Amnesty kan lalata da mata a gidajen yarin Maiduguri-2:30"