A cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, yanzu haka jami’an tsaro suna ta kokarin ganin sun tattara ‘yan matan guri guda domin a tantance lafiyarsu.
Fadar shugaban kasar dai bata bayar da wani cikakken bayani ba kan yadda aka samu ceto ‘yan matan ba.
Duk da yake dai gwamnati bata bayar da bayani kan cewa yadda aka kubutar da ‘yan matan ba, masana tsaro na ganin cewa dole ne a yi taka tsan-tsan.
Dakta Kabiru ‘Dan Ladi Lawanti, na jami’ar Ahmadu Bello na ganin cewa sako ‘yan matan abu ne mai kyau, amma kuma hatsarin dake tattare da hakan shine idan har gwamnati ta biya kudi ne aka saki ‘yan matan, hakan zai jefa sauran yara ‘yan makaranta cikin hatsari.
Sai dai kuma kungiyar Amnesty International ta ce tana farin cikin ganin an sako ‘yan matan, amma kuma tana nan kan bakanta na ganin an gudanar da bincike kan yadda tun farko aka sace ‘yan matan.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5