Ana cigaba da takaddama tsakanin masu rinjaye dake da gwamnati da 'yan adawa dake rike da kujerar kakakin majalisar dokokin kasar Niger wanda ake kokarin tsigewa
WASHINGTON, DC —
A majalisar dokokin kasar Nijer ana cigaba da takaddama tsakanin masu rinjaye dake da gwamnati da kuma 'yan adawa dake rike da kujerar kakakin majalisar kasar.
Yunkurin tsige kakakin majalisar Hamma Ahmadu da masu rinjaye suka yi domin sun ce bai dace dan adawa ya zama shugaban majalisar ba shi ya kawo wata mummunar takaddamar da majalisar ke fama da ita yanzu. Kawo yanzu dai bangarorin biyu sun kashe dare suna kai ruwa rana dangane da irin matakin da su masu rinjaye zasu dauka su cimma burinsu. Haka ma su ma 'yan adawa suna nan suna nazarin yadda zasu cigaba da rike kujerar kakakin.
Burin masu rinjaye shi ne su ture Hamma Ahmadu wanda tsohon firayim ministan kasar ne daga kujerar kakakin majalisar dokokin. 'Yan adawa kuma suna neman kariya mafi karfi su kare madugunsu.
Duk da takaddamar dake gudana kakakin Hamma Ahmadu yace shi bai taba yiwa wani barna ba amma babu wanda zai iya kawo hujja yace ga abun da shi yayi. Dangane da yunkurin tsigeshi a zaman majalisar da zasu yi Hamma yace komi yana hannun Allah. Allah ke bada mukami shi ne kuama yake karbewa. Sabili da haka shi bashi da wata fargaba akan kowane mataki majalisar ta dauka.
Bangaren gwamnati na zargin shi Hamma Ahmadu da yin wasu abubuwa da basu dace ba da kuma suka zarce yin adawa tare da yin kokakrin gurbata tafiyar mulkin jamhuriya ta bakawai.
Malam Bazu Muhammed shugaban jam'iyyar PNDS Tarayya kuma ministan harkokin wajen kasar ta Niger yana ganin irin halayyar Hamma Ahmadu yanzu basu cancanta ba. Yace idan Hanmma Ahmadu na yin nazari bai kamata ya raina PNDS Tarayya ba. Yace wani yana iya ya rainasu amma bashi ba. PNDS ce ta cireshi daga gidan kaso ta mayarda shi mutum bai kamata ya yi masu raini ba.
Yau da safe majalisar zata cigaba da zamanta. Ba'a san yadda zata kaya ba sai 'yan majalisar sun zauna domin sun watse ne baram baram a taronsu na shekaranjiya.
Ga rahotob Abdullahi Mamman Ahmadu

Your browser doesn’t support HTML5