Batun zaben 'yan tinke ya taso ne a jam'iyyar APC mai mulki inda PDP mai adawa za ta ci gaba da anfani da wakilai a zaben fidda gwani.
Tsarin fitar da gwani kai tsaye bai samu karbuwa ba a jam'iyyar APC, musamman tsakanin gwamnoninta baicin na tsayar da shugaban kasa wanda tamkar tabbatar wa shugaba Buhari tikitin tsayawa ne. Gwamnonin sun amince da yin anfani da waikai ko kuma tsayar da wadanda suka fi kwanta masu a rai.
Amma a gefe guda wadanda ba sa danyen ganye da gwamnonin na cewa lallai sai an yi masu zaben 'yan tinke domin a tabbatar da an yi adalci.
Sabo Usman Jama'are tsohon dan majalisar wakilai dake cikin tawagar Bauchi sun yi dafifi a hedkwatar jam'iyyar APC domin yada manufarsu. Ya ce " muna kira ne a kan gaskiya. Idan za'a yi gaskiya shi ne kawai kowa halinsa da sallarsa ta fitar dashi...Idan mutum ya yi dede zai ga dede, idan bai gani ba, ba gwamnan ba kodashi wanene hali ne kawai zai fitar da mutum". A cewarsa kiran da shugaba Buhari ya yi na cewa a bi gaskiya idan ba'a yi hakan ba to duk shiririta ne. Shugaba Buhari da shugaban jam'iyyar, Adam Oshiomhole su na son a yi 'yan tinke amma gwamnoni ne ba sa son a yi zaben fidda da gwani kai tsaye, wato kato bayan kato.
A jam'iyyar PDP kuma wasu masu son tsayawa takara na ci gaba da sayen takardar tsayawa cikinsu ko har da wani tsohon minista Adamu Maina Waziri na jihar Yobe mai son tsayawa takarar kujerar Sanata maimakon mukamin gwamna da ya saba nema. A cewarsa daga 1998 sau biyar ya nemi tsayawa dan takara amma sau biyu kawai ya ci nasara. Sai dai a zabukan da ya tsaya ya fadi.
Sanadiyar ba matasa damar a dama dasu a harkokin tsayawa takara ta sa a wannan karon Adamu Maina Waziri zai nemi takarar kujerar Sanata da fatan Allah zai ba matshi mai kishin jiharsa ta Yobe daga jam'iyyarsa damar zama gwamnan jihar.
Ko menene ma ya faru Adamu Maina Waziri ya ce ba zai canza sheka daga PDP zuwa wata jam'iyya ba domin masu yin hakan muradun kansu ne su ke bi.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5