KANO, NIGERIA - A wata hira ta talabijin ranar Litinin din nan, Sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya ce aikin rusau din da gwamnatin jihar ke yi na daga cikin yunkurin ta na kwato filaye mallakar kamfanoni da cibiyoyin gwamnati da suka zargi gwamnati mai shudewa da baiwa mutane mallaka.
Wasu alkaluma da aka fitar cikin karshen mako sun nuna wadanda rusau din gwamnatin Kano ya shafa sunyi asarar a kalla Naira biliyan 120 cikin makonni uku.
Engr. Rabiu Said Darakta a kamfanin da suka yi yarjejeniya da gwamnatin da ta gabata wajen sake gina Otel Daula na Kano wanda gwamnatin Kanon ta yanzu ta rusa ya ce “zamu dauki mataki na shari’a, da ma mun lissafa abin da muka kashe Naira biliyan goma ne kuma zamu nemi hakkin mu a Kotu, tuni muka umarci lauyoyin mu su karbo mana hakkin a wajen gwamnatin jihar Kano a zauren kotu”
Baya ga Otel Daula, gwamnatin ta rusa shaguna a bakin Masallacin Idi na Kano da wasu a filin Race Course da wani bangaren gidaje a yankin unguwar Salanta Daura da Yahaya Gusau Road, har ma mamallaka wadanann wurare ke cewa, “ba za mu iya misalta halin damuwar da muke ciki ba, mun cika dukkanin ka’idoji da gwamnati ta shimfida kuma muna da takardun mu a hannu, mun biya dukkannin kudaden ka’ida na gwamnati” a cewar wani da gwamnati ta rusawa gida yana ciki da iyalan sa mai suna Ali Rabiu.
Koda yake gwamnatin ta Kano na ikirarin cewa, yaki take na farfado da kadarorin gwamnati da ta ce gwamnatin baya ta mallakawa wasu mutane, amma masana dokoki da shari’a a Najeriya na cewa dole za ta bi ka’ida.
“Duk dan kasa na da hakkin mallakar kadara ta gida ko fili kuma gwamnati nada ikon karba, amma tilas sai an sanar da cewa, gwamnati na son wurin ta kuma sanar da shi amfanin da za’ayi da fili kana kuma a biyashi diyya, haka kundin tsarin mulkin kasa ya shimfida kuma abin da dokar mallakar kasa ta shata kenan” a cewar Barrister Garba Abubakar, wani lauya mai zaman kansa a Dutse, jihar Jigawa Najeriya.
Yayin da wasu daga cikin wadanda wannan rusau ya shafa ke cewa, sun tunkari kotu domin neman hakki, wasu Jama’a kuwa na ganin kamata yayi ace dattawan Kano da sauran masu ruwa da tsaki sun shiga tsakani domin samun daidaito, da nufin kubutar da Kanon daga fadawa cikin yanayin rundani ta fuskar harkokin saka jari da hada-hadar kasuwanci.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5