Ana Shirin Gudanar Da Sulhu A Rikicin Kasar Yemen

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffith, ya ziyaranci kasar Yemen domin shirin tattaunawar zaman lafiya.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin Yemen, Martin Griffith, yana ziyara a kasar ta Yemen, domin share fagen tattaunawar zaman lafiya da ake shirin yi.

Ziyarar na zuwa ne, yayin da wani sabon fada ya barke a farkon makon nan a birnin Hodieda.

An shirya cewa, Griffith zai hadu da Jami’an Houthi da ke samun goyon bayan Iran, a wani yunkuri na shawo kan su da gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya, domin su hau teburin tattaunawa a kasar Sweden kafin karshen shekarar nan.

A ‘yan kwanakin nan, bangarorin biyu sun amince da gayyatar ta Griffith, amma rahotanni sun ce, barkewar sabon rikicin da aka samu a kwana nan, zai iya kawo cikas ga kokarin sulhunta bangarorin biyu.