BAYELSA: Ana Sake Zaben Gwamnan Bayelsa a Wasu Kananan Hukumomin Jihar

Wata Na'urar Tantance Mai Kada Kuri'a

A yau ne ake sake zaben wasu kananan hukumomi irin su Ijaw ta Kudu da Ikirimo da Amasoma a jihar Bayelsa a zaben gwamnan da aka soke a baya. Ijaw ta Kudu dai mafi yawancinta tana kan ruwa ne fiye da tsandauri.

An ta samu karar harbe-harbe a wasu sassa na karamar hukumar Ijaw ta Kudu inda ya bar masu kada kuri’a cikin dar dar din yin zaben.

To amma a wasu kananan hukumomin kuma zaben na tafiya ba laifi. Haka kuma a wasu wuraren an sami matsalar sata ko fauce akwatunan zaben da aka tulawa kuri’un da aka kada.

Jami’an tsaro sun yi iyakar kokarinsu don tarwatsa wasu ‘yan dabar siyasa da suka so tada hankali a karamar Hukumar Amasoma ta jihar. Haka zalika yawancin karar harbe-harben da aka ji a wurare na da nasaba kokarin kawo cikas a zaben.

Wakilinmu Lamido Abubakar Sakkwato ne ya zagaya lungunan jihar don ganewa idanunsa yadda zabben ke tafiya a kokarin sake zaben wuraren da hukumar zaben Najeriya INEC ta soke sakamakon wasu magudi da aka yi a baya na zaben gwamnan jihar.

Your browser doesn’t support HTML5

BAYELSA: Ana Sake Zaben Gwamnan Bayelsa a Wasu Kananan Hukumomin Jihar - 4'01"