Tashar jirgin kasa ta Rigasa dai ta zama dandalin daru a 'yan kwanakin nan saboda yadda wasu matafiya kan kwashe yini ba tare da sun sami tafiya Abujan ba.
Wasu daga cikin matafiya dai na ganin son rai ne ke kawo cunkoson; wasu kuma na danganta matsalar da tabarbarewar tsaro. Mallam Mohammed da ya yini a tashar jirgin ya ce ya yi iya kokarinsa domin ya samu tikiti amma kuma abu ya ci tura, lamarin da ya alakanta da yawan cunkoson matafiya a tashar.
Wasu mata da su kuma suke neman tikiti sun yi korafi kan gaza samun tikitin tafiya Abuja, inda su ke zargin cewa ana cuwa cuwar tikitin, kana wasu kuma sun saye tikitin amma kuma jirgi ya tashi ya bar su.
Kokarin jin ta bakin jamai'an hukumar jiragen kasan da ke Rigasa dai ya ci tura saboda sun ce ba a basu ikon magana da 'yan jaridu ba. Sai dai wani ma'aikaci da ya boye sunan shi ya ce cunkoson dai ya samo asali ne daga matsalar tsaro.
Jirgin kasan dai kan tashi daga Kaduna zuwa Abuja kullum da safe, rana, da yamma amma duk da haka wasu matafiya kan yini ba tare da sun samu lafiya ba.
Ga dai rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:
Your browser doesn’t support HTML5