A cikin hirar shi da Sashen Hausa, gwamna Masari yace bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu na nuni da cewa, wadansu yaran suna makwabciya jihar Zamfara inda aka sa su ayyuka sai dai yace kawo yanzu ba za a iya bada cikakken bayani kan yanayin da yaran suke ciki ko kuma matakan da ake dauka na ceto su sabili da dalilai na tsaro.
Gwamna Masari ya bayyana cewa gwamnati ta kafa cibiyar samar da bayanai da suka samar da lambobin za da za a iya aika sakonni ko kuma bayar da bayanai da zasu taimaka wajen ceto daliban. Cibiyar zata kuma rika samar da bayanai ga manema labarai kan halin da ake ciki.
yadda-daya-daga-cikin-daliban-da-aka-sace-a-katsina-ya-kubuta
sojojin-najeriya-sun-gano-inda-wadanda-suka-sace-dalibai-a-katsina-suke
iyaye-a-katsina-sun-yi-zanga-zangar-neman-a-ceto-ya-yansu
Ya kuma kara kira ga iyaye su ci gaba da hakuri da addu’oi yayinda gwamnati ke iyakar kokarin ceto ‘yan makarantar. Ya kuma yi alkawarin daukar dukan matakan da suka kamata na tabbata cewa haka bata sake faruwa a makarantu ko kuma wuraren tarukan jama’a da mata da kananan yara su ke zuwa ba.
Tun farko gwamnan Masari ya kai ziyarar gani da ido a makarantar da aka sace daliban kashe garin aukuwar lamarin, tare da bada umarnin rufe dukannin makarantun kwana a jihar domin gudun sake afkuwar lamarin, yayinda kuma ya yi tattaki domin yi wa shugaba Muhammadu Buhari bayani kan halin da ake ciki.
Tuni kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai harin sai dai kawo yanzu, gwamnatin tarayya bata maida martani dangane da ikirarin Abubakar Shekau shugaban kungiyar na kai harin ba.
Saurari hirar da Sani Shu’aibu Malumfashi ya yi da gwamna Masari.
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, Masari, da jihar Katsina.