Kamar yadda ake anfani da wasu karnuka na musamman wajen gano nakiyoyi haka wani mai bincike ya gano cewa ana iya yin anfani da karnukan wajen gano yanayin mai cutar sukari
WASHINGTON DC —
Masana suna nazarin yadda za'a iya amfani da karnuka irin wadanda ake horaswa su gano nakiyoyi ko wasu abubuwa masu hadari,haka nan ana iya horasda da su su gano idan masu cutar sukari suna fuskantar hadari idan sukarin yayi kasa ko ya haura a jikin dan'Adam.
Wanda ya gano da wannan hikimar,wani masanin kimiyyar bincike ne Mark Ruefenacht,yace kudin horasda ko wane irin wannan kare zai kai dalar Amurka dubu hamsin, watau kimanin Naira miliyan 20.
Tuni har an rarraba irin wadannan karnukan su dari ga masu fama da cutar sikari. Suna fatan fadada wannan shiri.
Akwai kamfanonin bincike da suka so saye wannan bincike amma Mark yaki.